Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Daga Bayyananniyar Hujja Zuwa Aiwatarwa
In sha Allah kamar yadda a rubutun baya mu kai magana kan ci gaba da kawo fassarar rubutun maƙala mai taken "Me Ya Sa Wilayatul Faƙih Buƙata Ce ta Hankali", bayan gabatarwar maƙalar yanzu za a shiga cikin ta. Da fatan masu karatu za su amfana da ita.
Sashe na Farko: Me Ya Sa Muke Buƙatar Waliyyin Faƙih a Zamanin gaibar Imam?
Dalilan Hankali Ga Kowa
Shin Al’umma Za Ta Iya Rayuwa Ba Tare da Shugaba Ba?
Mu fara da tambaya mafi sauƙi:
“Shin mutane da yawa da suka makale a wani tsibiri, za su iya ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali ba tare da wani shugaba ba?” Hankali yana cewa: A’a! Domin kowane mutum zai mayar da hankali kan kansa, za a iya take haƙƙin wasu, sannan saɓani ya rikide zuwa yaƙin cikin gida. Wannan wata ƙa’ida ce ta dabi’ar rayuwar zamantakewar mutane.
Alƙur’ani ma ya yi nuni da wannan ƙa’ida ta hankali, inda Allah Ya ce:
«وَ لَوْ لا دَفْعُ اللَّهِ النَّاسَ بَعْضَهُمْ بِبَعْضٍ لَفَسَدَتِ الْأَرْضُ»
“Da Allah bai kare wasu mutane daga wasu ba, da ƙasa ta lalace.” (1)
Ma’anar hakan ita ce, domin hana lalacewa da rikice-rikice, dole ne a samu wani ƙarfi mai hana zalunci a cikin al’umma, wanda zai dakatar da zalunci da take haƙƙoƙin mutane. Wannan ƙarfi mai hana zalunci shi ne gwamnati.
Saboda haka, buƙatar gwamnati wata ƙa’ida ce ta hankali bayyananniya, wadda babu wata al’umma da za ta iya samun kwanciyar hankali ba tare da ita ba.
Idan Gwamnati Ta Musulunci ce, Me Ya Sa Shugabanta Zai Kasance Faƙihi?
Yanzu mu ɗauka cewa wata al’umma ta kasance al’umma ce ta Musulunci, wato mutanenta sun amince cewa dole ne su gudanar da rayuwarsu bisa dokokin Musulunci.
Tambayar ita ce: “Shin kowa zai iya zama shugaban wannan al’umma?” Hankali yana cewa: A’a!
Domin idan shugaban bai san dokokin Musulunci ba, ba zai iya yin hukunci bisa waɗannan dokoki ba. A sakamakon haka, gwamnatin Musulunci za ta koma gwamnati mai dogaro da ra’ayin mutum.
Allah Maɗaukaki Ya ce:
«وَ أَنزَلْنَا إِلَیْکَ الذِّکْرَ لِتُبَیِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَیْهِمْ»
“Mun saukar maka da Ambato domin ka bayyana wa mutane abin da aka saukar musu.”(2)
Wannan yana nufin cewa Manzon Allah (S.A.W.A) ya zo ne domin ya bayyana dokokin Allah ga mutane.
Saboda haka, mutumin da zai jagoranci al’umma a madadin Manzon Allah (S.A.W.A) a zamanin gaibar Imam, dole ne ya kasance yana da ikon sanin waɗannan dokoki da aiwatar da su a cikin al’umma. Irin wannan mutum, wanda ya ƙware wajen sanin dokokin Musulunci, ana kiransa Faƙih.
Saboda haka, hankali yana cewa: Idan gwamnati ta Musulunci ce, shugaban ta ya kamata ya kasance Faƙihi, wato masani kan dokokin Musulunci, mai adalci kuma mai iya aiwatar da su.
A Zamanin Gaibar Imam, Wa Ya Kamata Ya Yi Mulki?
Mun san cewa a Musulunci, Allah ne mai cikakken ikon mulki, sannan Manzon Allah (S.A.W.A) da Imamai Ma’asumai (A.S), waɗanda Allah Ya naɗa.
Amma tambayar ita ce: “A zamanin gaibar Imam Zaman (A.F), lokacin da ba mu da damar zuwa ga Imam Ma’asumi kai tsaye, mene ne ya kamata mu yi? Shin mu bar al’umma ba tare da jagora ba, har rikice-rikice su auku?”
A nan ne hankali yake shiga ya ce: “Idan Allah Ya naɗa mutum Ma’asumi domin gudanar da al’umma a cikin shekaru ɗari biyu na farko na Musulunci, kuma har yanzu muna da irin waɗannan buƙatu, shin ya dace a ce Allah Ya bar mu ba tare da jagora ba?”
A’a! Wannan bai dace da hikimar Allah ba. Saboda haka, Allah Ya sanya wasu siffofi a cikin wasu bayinsa waɗanda za su iya maye gurbin Imam Ma’asumi. Waɗannan siffofi su ne:
* Sanin dokokin Allah, wato Fikihu.
* Adalci.
An bayyana cewa akwai waɗannan siffofi a tattare da malamai da dama na zamanin gaibar Imam.
Imam Khumaini (R.A) ya ce: “Allah bai ayyana wani mutum na musamman domin mulki a zamanin gaibar Imam ba. Amma Ya tanadi wannan cancantar ta gudanar da mulki, wadda ta kasance tun farkon Musulunci har zuwa zamanin Sahibul Amr (A.F), domin ta ci gaba bayan gaibar Imam. Wannan cancanta, wadda ta ƙunshi sanin doka da adalci, tana tattare da malamai da yawa na zamaninmu.”
Saboda haka, hankali yana cewa ya kamata mu koma ga mutanen da suke da wannan cancantar gudanar da mulki, wato malamai masu ilimi da adalci.
Shin Hankali Yana Goyon Bayan Wilayatul Faƙih?
Dalilai Uku Masu Sauƙin Fahimta
Mu bincika wannan batu ta hanyar dalilai guda uku na hankali:
Dalili na Farko: Ka’idar Lutf (Rahamar Allah)
Allah a koyaushe yana yi wa bayinsa rahama, kuma ba Ya barin su ba tare da jagora ba wajen neman samun farin ciki da tsira. Idan a zamanin gaibar Imam wata al’umma ta kasance ba tare da shugaba mai adalci da ilimi ba, hakan bai dace da rahamar Allah ba.
Saboda haka, ya kamata Allah Ya bayyana mutanen da za su iya gudanar da aikin Imam a cikin al’umma. Wannan bayani ya zo ne ta hanyar siffofin ilimi da adalci.
Dalili na Biyu: Ci Gaban Aiwatar da Hukunce-hukuncen Musulunci
Musulunci addini ne da aka saukar domin kowane zamani. Idan a zamanin gaibar Imam ba za a iya aiwatar da hukunce-hukuncen shari’a ba, kamar dokokin hukunta laifuka da kare al’ummar Musulunci, hakan zai nuna cewa Musulunci ya takaita ne ga shekaru ɗari biyu kawai, wato zamanin Imamai Ma’asumai. Wannan bai dace da ayoyin Alƙur’ani ba, kamar:
«اَلْیَوْمَ أَکْمَلْتُ لَکُمْ دِینَکُمْ»
“A yau Na kammala muku addininku.”
Saboda haka, dole ne a samu wanda zai ci gaba da gudanar da waɗannan ayyuka a Zamanin gaibar Imam.
Dalili na Uku: Hanyar Masana da Mutane Masu Hankali
A cikin al’ummomin mutane, ana komawa ga ƙwararru wajen gudanar da muhimman al’amura. Misali, idan muka je wurin likita, muna zuwa ne saboda ƙwarewarsa a fannin magani.
Haka kuma, a harkar mulki, ya kamata a samu mutumin da yake da ƙwarewar gudanar da gwamnati bisa Musulunci. Wato, wanda ya san dokokin Musulunci, yake da adalci kuma yake da ƙwarewar gudanar da al’umma.
Saboda haka, ba wa Faƙihi wanda ya cika sharuɗɗa amanar mulki wani aiki ne da ya dace da hankali, kamar yadda ake ba ƙwararru muhimman ayyuka a cikin al’umma.
Amsa Ga Wata Shubuha: Shin Faƙihi Ma’asumi Ne?
Wasu mutane suna cewa: “Shin Faƙihi Ma’asumi ne da har za mu yi masa biyayya?”
Amsar hankali ita ce: Ba lallai ne biyayya ga Faƙih ta kasance saboda ana ɗaukarsa a matsayin Ma’asumi ba. A’a, ana yi masa biyayya ne a matsayin shugaba mai adalci da ƙwarewa. Wannan yana kama da yadda muke bin umarnin likita mai ƙwarewa wajen kula da lafiyarmu, ko kuma yadda muke amincewa da shawarar injiniya mai ƙwarewa wajen gina gida. A waɗannan misalan, muna bin su ne saboda ƙwarewarsu, amana da gaskiyarsu, ba saboda su Ma’asumai ba ne.
Haka ma yake a wajen Waliyyin Faƙih, ana bin sa ne saboda saninsa da dokoki da kuma adalcinsa. Wannan biyayya ba ta nufin ɗaukarsa a matsayin Ma’asumi.
Taƙaitaccen Bayani: Me Ya Sa Wilayatul Faƙih Ba Kawai Ra’ayi Ba Ne, Sai Dai Buƙata?
* Al’umma ba tare da shugaba ba za ta iya faɗawa cikin rikice-rikice. Wannan ƙa’ida ce ta hankali.
* Idan gwamnati ta Musulunci ce, shugaban ta ya kamata ya kasance Faƙih, wato masani kan dokokin Musulunci.
* A zamanin gaibar Imam, ba mu da damar zuwa ga Imam Ma’asumi kai tsaye, amma malamai masu adalci suna da wasu siffofin cancantar gudanar da mulki.
* Hankali yana goyon bayan Wilayatul Faƙih ta dalilan Lutf, ci gaban aiwatar da hukunce-hukuncen Musulunci da hanyar masana.
* Biyayya ga Waliyyul Faƙih tana nufin bin shugaba mai ƙwarewa da adalci, ba ɗaukarsa a matsayin Ma’asumi ba.
* Saboda haka, Wilayatul Faƙih buƙata ce ta hankali domin kare Musulunci, aiwatar da dokoki da hana rikice-rikice a Zamanin gaibar Imam.
Za mu ci gaba...
Ra'ayinka